3 Mayu 2020 - 05:35
Wani Sojan Kasar Faransa Ya Mutu Bayan Samun Raunuka A Kasar Mali

Gwamnatin kasar Faransa ta bayar da sanarwar mutuwar sojan kasar guda a ranar juma’ar da ta gabata a birnin Paris inda yake jinyar raunukan da ya samu a wata fafatawa da ‘yan ta’adda a kasar Mali.

(ABNA24.com) Gwamnatin kasar Faransa ta bayar da sanarwar mutuwar sojan kasar guda a ranar juma’ar da ta gabata a birnin Paris inda yake jinyar raunukan da ya samu a wata fafatawa da ‘yan ta’adda a kasar Mali.

Kamfanin dillancin labaran “Reuters” ya nakalto majiyar sojojin kasar ta Faransa tana cewa sojan mai suna Brigadier Dmytro Martynyouk yana aiki da runduna ta daya ta sojojin Faransa a yankin Sahel a ranar 23 ga watan Afrilun da ya gabata, inda ya taka nakiya wacce ta yi masa lahani sosai. Kuma tun lokacin ne yake jinya a birnin Paris, amma ranar juma’ar da ta gabata rai ya yi halinsa.

Gwamnatin kasar Faransa tana da sojoji 5,100 a yankin sahel tun shekara ta 2013 da sunan yaki da yan ta’adda masu kishin adddinin a yankin. A cikin watan Nuwamban shekaran da ta gabata ma sojojin kasar ta Faransa 13 ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin jirgin saman yakin kasar a kasar ta Mali.



/129